الخميس ، ٢٠ ربيع الآخر ، ١٤٤٨   -   01 أكتوبر 2026

Yini Da Dare Kammalallen Tsarin Yini Da Dare A Rayuwar Annabi Muhammad Sallallahu alaihi wa sallam

Yini Da Dare Kammalallen Tsarin Yini Da Dare A Rayuwar Annabi Muhammad Sallallahu alaihi wa sallam

Yini Da Dare

Yinin Annabi sallallahu alaihi wa sallam ba yini ba ne irin na gama gari da yake farawa da safe ya qare da yamma. A'a, yini ne da saboda yawan ayyukan da ke cikinsa ka xauka kowane lokaci shi ne farkonsa, saboda Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam mutum ne mai amfani da dama da kuma lokaci, yana xaukar duk wani minti ko awa abar lissafawa ce a wurin sa, don haka tana da amfaninta, haka kowane yini akwai aikin da za a yi a cikinsa, ajali kuma yana kafa rumfarsa a kan rayuwa, yana jira lokaci ya yi ya qare.

A cikin waxannan takardun littafin zamu rayu tare da Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam a safiyarsa da yammacinsa, zamu tafi kasuwa tare da shi, mu ci daga abin da Allah ya ba shi, mu ji muryarsa mai daxi yayin da yake koyarwa, da yayin da yake Sallah, mu zauna tare da shi a kan tabarmarsa, wadda yake zama a kai, mu ci xan abincin da aka tanada masa.

Zaka iya shiga gidan Annabi sallallahu alaihi wa sallam ta hanyar siffaita shi da sahabbai suka yi, kuma za ka iya ganin natsuwarsa yayin da yake barci, ka ga nishaxinsa yayin da yake zaune, wataqila ma ka ga jariri a kan cinyarsa, ko yaro xan qarami a kan bayansa, ya samu ximin jikinsa da albarkarsa.

Ta yaya wannan mutum mai girma irin Annabi sallallahu alaihi wa sallam yake mu'amala a matsayinsa na mutum da kuma saqon da aka aiko shi da shi?

Yaya yake mu'amala da lokacinsa na yau da kullum?! Yaya yake qare ranakunsa?! Me yake yi a cikinsu?!

Wannan shi ne bayanin yini guda na Annabi sallallahu alaihi wa sallam Manzo, mutum, wanda yake da nauyi a kansa, uba, miji, aboki. Wannan shi ne "Yinin Annabi sallallahu alaihi wa sallam" shi ne wannan littafin da yake gabanka.

Abdulwahhab Axxurairí

 تنزيل
نشر :